Nijeriya Ta Zama Kasa Ta 3 Da Ta Fi Karbar Bashin Bankin Duniya

Nijeriya ta zama ƙasa ta uku wajen karbar bashin Bankin Duniya bayan karuwar karbar rancen sama da dala biliyan biyu daga 2023 zuwa 2024. Karuwar

Nijeriya ta zama ƙasa ta uku wajen karbar bashin Bankin Duniya bayan karuwar karbar rancen sama da dala biliyan biyu daga 2023 zuwa 2024.

Karuwar wannan kaso ne ya sanya Nijeriya ta zama kasa ta uku a duniya ta tafi karbar bashin Bankin Duniya.

A cewar bankin, kasar Bangladesh na ci gaba da rike matsayinta na farko a matsayin mafi cin bashin bankin duniya, inda bashin da ta karba ya karu daga dala biliyan 19.3 a 2023 zuwa dala biliyan 20.5 a 2024.

Pakistan na rike matsayinta na biyu da adadin bashin da ya kai dala biliyan 17.9.

Sai kasar Indiya da ta ke matsayi na uku a baya ta samu rage bashin da ake binta daga dala biliyan 17.9 a 2023 zuwa dala biliyan 15.9 a 2024 abin da ya sa Nijeriya ta maye gurbinta.

Bayanai daga ofishin lura da basuka kasa, ya nuna cewar bashin da Bankin Duniya ke bin Nijeriya ya kai dala biliyan 15.59 a watan Maris na 2024.

Wannan na zuwa daidai lokacin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke kara dogara da tallafin kudi daga kasashen waje yayin da ake fuskantar matsin tattalin arziki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments