Nijar ta kulla yarjejeniyar sayen tauraron dan adam da na’urar radar daga Rasha

Jamhuriyar Nijar ta cimma yarjejeniya da kamfanin Glavkosmos na kasar Rasha a wannan  Juma’a kan sayen tura tauraron dan adam na sadarwa, da kuma na’urar

Jamhuriyar Nijar ta cimma yarjejeniya da kamfanin Glavkosmos na kasar Rasha a wannan  Juma’a kan sayen tura tauraron dan adam na sadarwa, da kuma na’urar radar domin ayyukan tsaro.

Wannan hadin gwiwar  wanda ke da nasaba da tattaunawar da aka yi a Mali a watan Satumba, ya kunshi daidaitawa tsakanin sabuwar Kungiyar Kasashen Sahel (AES) wanda ya hada da Mali, Nijar, da Burkina Faso – da kamfanin Glavkosmos, wanda bangare ne na kamfanin gwamnatin Rasha Roskosmos.

Ministan Tattalin Arziki da Kudi na Mali Alousseni Sanou ne ya sanar da cewa, shirin na AES zai hada da samar da tauraron dan adam na sadarwa da aka kera don inganta hanyar sadarwa ta intanet a yankuna masu nisa, da kuma tauraron dan adam domin ayyukan tsaron kan iyaka, da sarrafa albarkatun kasa, da kuma ba da taimako a kokarin magance bala’o’i.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital na Jamhuriyar Nijar, Sidi Mohamed Raliou, ya bayyana cewa wadannan sabbin tsare-tsare sun ta’allaka ne kan samun ‘yancin kai a fannin sadarwa da tsaro.

Manufar  ita ce baiwa kasashen AES uku damar samun dabarun sarrafa bayanansu da ayyukan tauraron dan adam.

“Mun amince da kamfanin na Rasha kan sayen wadannan tauraron dan adam guda uku na tsawon shekaru hudu,” in ji Ministan na Nijar, yana mai cewa Mali ta riga ta kammala wannan yarjejeniyar da kamfanin na Rasha.

Nijar dai ta kara karfafa alakarta da Rasha ne biyo bayan da alakarsu ta yi tsami da Faransa wadda ta yi mata mulkin mallaka na tsawon shekaru.

Jamhuriyar Nijar na da arzikin ma’adanai na karkashin kasa, da suka hada da zinariya, danyen man fetur da arzikin sanadarin uranium, kamar yadda kuma take da arzikin fadin kasa da kuma noma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments