A wannan Labara ce Allah ya yi tsohon dan siyasa kuam tsohon firayi ministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou rasuwa.
Hukumomin Nijar sun sanar da cewa Hama ya rasu ne a asibitin birnin Yamai fadar mulkin Jamhuriyar Nijar bayan jinya.
Hama Amadou wanda ya yi ficea fagen siyasar Nijar, an haife shi ne a Youri a shekarar 1950.
Ya zama firaminista har sau biyu daga 21 ga watan Fabrairun 1995 zuwa 27 ga Janairun 1996 a karkashin mulkin Mahamane Ousmane sai kuma a lokacin mulkin Mamadou Tanja ya sake rike wannan matsayi tun daga 31 ga Disambar 1999 zuwa 7 ga Yunin 2007.
Sai kuma a shekarar 2011 aka zabe shi a matsayin shugaban majalisa, kuam ya ci gaba da zama kan wannan matsayi har zuwa 2013, haka nan kuma ya tsaya takarar shugaban kasar Nijar a 2016, duk kuwa da cewa abokin karawarsa Mahamadou Issoufou ne ya yi nasara a zaben.