Netanyahu Ya Soki Macron Kan Kiran Da Ya Yi Na A Daina Baiwa Isra’ila Makamai

Firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya caccaki shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan kiran da ya yi na kawo karshen bai wa haramtacciyar kasar

Firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya caccaki shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan kiran da ya yi na kawo karshen bai wa haramtacciyar kasar Yahudu makamai, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyar Hizbullah da Iran.

A wata hira da ya yi da kafofin yada labaran Faransa da aka watsa a wannan Asabar, Macron ya yi kira da a samar da mafita ta siyasa kan rikicin yankin gabas ta tsakiya, ya kuma ce ya kamata kasashen yammacin duniya su daina kai makaman yaki a Gaza.

Ya kira ci gaba da tashin hankalin a matsayin babban kuskure,  kuma ya yi gargadi game da mayar da Lebanon zuwa wata “sabuwar Gaza.”

Netanyahu ya mayar da martani a wata sanarwa mai zafi a kan dandalin X , inda yake  magana da Macron kai tsaye.

Ya ce Isra’ila tana yaki ne a bangarori bakwai da abokan gaba masu wayau, in ji shi, yayin da yake magana game da rikice-rikicen da Isra’ila ke yi da Hamas, Hizbullah, Houthis, da kuma Iran gami da kawayenta a Siriya da Iraki.

Netanyahu ya ce”Ya kamata dukkan kasashen da ke da wayewa su tsaya kyam a bangaren Isra’ila.” Yana mai cewa kalaman Macron dangane yakin Isra’ila da kuma yin kirada a daina bata makamai babban abin kunya ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments