Najeriya : Kotu Ta Aika Masu Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati Gidan Yari

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta aika da mutum 10 wadanda ake zargi da hannu a zanga-zangar kin jinin gwamnati zuwa gidan yari. Mai shari’a

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta aika da mutum 10 wadanda ake zargi da hannu a zanga-zangar kin jinin gwamnati zuwa gidan yari.

Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya ya aika da maza tara gidan gyaran hali na Kuje sannan ya aika da mace daya zuwa gidan yarin Suleja.

Haka kuma alkalin ya saka ranar 11 ga watan Satumba a matsayin ranar da zai yanke hukunci dangane da buƙatar bayar da belin da wadanda ake zargin suka shigar a gaban kotun, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

Aika su gidan yarin na zuwa ne bayan an gabatar da su a gaban kotu inda ake tuhumar su da cin amanar kasa da yi wa gwamnati bore da kuma yunkurin hargitsa Najeriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments