Majalisar Hulda da Musulman Amurka, CAIR, kuma babbar kungiyar kare hakkin Musulmai a Amurka, ta ce tilas ne gwamnatin Biden ta dauki mataki bayan da Isra’ila ta sanar da sake ƙwace kasar Falasdinu a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye tare da kashe wasu fararen hula a Gaza.
Isra’ila ta sanar da ƙwace kusan kadada 2,000 ta kasar Falasdinu kusa da garin Salfit da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
“Ci gaba da yin shiru da gwamnatin Biden ke yi kan kisan kiyashin da ake yi a kullum da sauran laifukan yaki a Gaza, da kuma batun mamaye Yammacin Kogin Jordan, yana aike wa da gwamnatin Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi cewa ba za ta taba daukar alhakin duk wani mataki da ta dauka ba, komai rashin dacewarsa a doka, “in ji Mataimakin Daraktan CAIR na kasa Edward Ahmed Mitchell.
“Dole a kawo ƙarshen wannnan shirun na kisan ƙare dangi.”