Mukaddashin Shugaban Kasar Iran Muhammad Mukhbir Ya Mika Ofishin Shugaban Kasa Ga Shugaba Pezeskiyan A Yau Lahadi

Mukaddashin shugaban kasar Iran, ko shugaban kasar riko na gwamnatin marigayi ra’isi, Muhammad Mukhbir ya mika ofishin shugaban kasa ga sabon shugaban kasa Masoud Pezeskiyan,

Mukaddashin shugaban kasar Iran, ko shugaban kasar riko na gwamnatin marigayi ra’isi, Muhammad Mukhbir ya mika ofishin shugaban kasa ga sabon shugaban kasa Masoud Pezeskiyan, bayan da aka kammala bikin tabbatar da shi a matsayin zabebben shugaban kasar Iran a yau Lahadi 28 ga watan Yulin shekara ta 2024.

A bisa doka ta 9 daga asalin doka ta 110, na kundin tsarin JMI, jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khamani’e ya mikawa Masoud Peszeskiya shaida zamansa shugaban kasa na 9 bayan kafa JMI  shekara 45 da suka gabata.

Manya manyan jami’an gwamnati da jami’an diblomasiyya mazauna Tehran da manya manyan Jami’an sojoji da iyalan shahidai kimani 2,500 ne suka halarci taron tabbatar da Pezeskiyan a matsayin shugaban kasa daga waliyul Fakih, wato Imam sayyid aliyul Khaminaee.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments