Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Amman da kasarJordan a safiyar yau Laraba, a ci gaba da rangadin da yake a kasashen yankin Asiya ta kudu don ganin an kawo karshen kissan kiyashin da sojojin HKI suke yi a kasashen Falasdinu da Lebanon.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa ana saran ministan zai gana da manya manyan jami’an gwamnatin kasar ta Jordan, wadanda suka hada da tokwaransa na kasar Jordan Aiman Safadi da sauran manya manyan jami’an gwamnatin kasar.
Kafin tashin Aragchi zuwa kasar Jordan dai, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Baka’e ya rubuta a shafinsa na X kan cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar ba zata daina kokarin da take yi na ganin an kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa a a Gaza fiye da shekara guda ba, da kuma wadanda take aikatawa a kasar Lebanon.
Bakae ya kara da cewa ministan harkokin wajen kasar , bayan kasar Jordan dai, zai ziyarci kasashen Masar da Turkiyya don cimma wannan manufar. Ana saran Abbas Aragchiu zai tattauna da jami’an gwamnatin wadan nan kasashe don sanin yadda za’a bullowa matsalolin tsaro na yankin.
Kafin haka dai ministan ya je kasashen< Lebanon, Siriya, Omman, Qatar da kuma Saudiya.