Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya tattauna da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a Riyadh.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X cewa, “Dukkanin bangarorin biyu sun yi kira da a dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza da Lebanon da kuma kai agajin gaggawa ga ‘yan gudun hijira da suka kauraewa muhallansu.
Ministocin biyu sun kuma yi nazari kan halin da alakar kasashen biyu ke ciki a halin yanzu, tare da jaddada kudurinsu na karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban na siyasa, tsaro da tattalin arziki a tsakanin Iran da Saudiyya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Araghchi ya isa babban birnin kasar Saudiyya a wannan Laraba domin tattaunawa kan hanyoyin kawo karshen yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma hare-haren da take kaiwa Lebanon.
Araghchi ya yi ishara da ziyarar da ya yi a Lebanon da Syria a baya-bayan nan. Ya jaddada wajabcin dakatar da ayyukan soji na Isra’ila nan take a Gaza da Lebanon a matsayin mataki mai matukar muhimamnci domin domin hana barkewar tashe-tashen hankula a daukacin yankin.
Ministan na Iran ya yi kira da a hada dukkan karfin siyasa da karfin kasashen yankin don dakile kisan gillar da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da lalata ababen more rayuwa a Gaza da Lebanon.
Yarima Faisal ya jaddada manufar kasashen biyu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, yana mai bayyana shirin Saudiyya na yin hadin gwiwa ta wannan hanyar.
A yayin ganawar, Araghchi ya sake jaddada aniyar kasar Iran na ci gaba da fadada dangantakarta da kasashen dake makwabtaka da ita don inganta tsaro, kwanciyar hankali, da ci gaban kasashen yankin.
Ya kuma yaba da aiwatar da yarjejeniyoyin da kasashen Iran da Saudiyya suka rattabawa hannu a kansu.
Ministan harkokin wajen kasar ta na Saudiyya ya kuma bayyana aniyar kasarsa na ci gaba da aka samu a shekarar da ta gabata wajen karfafa alakar kasashen biyu na Iran da Saudiyya.
Miministan harkokin wajen na Iran ya gana da yarima mai jiran gado Mohammad bin Salman a birnin Riyadh, inda suka tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da kuma wajabcin yin aiki kafa da kafada da kafa tsakanin Iran da Saudiyya da sauran kasashen yankin, domin shawo kan lamarin da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.