Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Ma’aikatarsa Na Hada Kai Da Sojojin Kasar Don Maida Martani Kan Kissan Haniya A Cikin Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Aragchi yace ma’aikatarsa tana bada cikekken hadin kai ga sojojin kasar don ganin kasar ta maida martani kan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Aragchi yace ma’aikatarsa tana bada cikekken hadin kai ga sojojin kasar don ganin kasar ta maida martani kan kissan da HKI ta yiwa shugaban kungiyar Hamas Shahid Isma’il Haniya a birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyid Aragchi yana fadar haka a yau Asabar a ma’aikatar harkokin wajen kasar, a kuma rana ta farko na fara aiki a matsayin ministan harkokin wajen kasar.

Da farko Sayyid Aragchi ya yi addu’a wa Dr Hossain Amir Abdullahiyan, wanda ya gaba bayan rasuwarsa a cikin hatsarin jirgin sama a cikin watan Mayun da ya gabata.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin JMI zata ci gaba da goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma kawancen masu gwagwarmaya a yankin. Kuma wannan na cikin ganshikan tsarin JMI na harkokin wajen.

Dangane da yarjeniyar JCPOA ta shirin nukliyar kasar Iran kuma, Sayyid Aragchi ya bayyana cewa, babu gaggawa a cikin sa, Iran ta cika alkawulan da suka hau kantan dangane da yarjeniyar, amma kasashen yamma sun saba alkawulansu, kuma Amurka ta ma fice daga yarjeniyar. Don haka iran ta dauki matakan da suka dace bayan wannan saba alkawula.

Amma a halin yanzu gwamnatin kasar Iran zata hada biyu duka, zata ci gaba da bude kofa, saboda tattaunawa, duk da cewa yayi imani yarjeniyar JCPOA ba zata sake farfadowa ba saboda dalilai da dama, sannan zata yi ayyuka don ganin tasirin takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasar ya ragu. Daga karshe Iran ba zata taba saryar da hakkinta na mallakar fasahar nukliya ba.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments