Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Amurka Tana Hada Kai Da ‘Yan Sahayoniyya Wajen Tada Hankula

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kasancewar Amurka tare da ‘yan sahayoniyya wajen haifar da tashin hankali a yankin Gabas taTsakiya ya bayyana

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kasancewar Amurka tare da ‘yan sahayoniyya wajen haifar da tashin hankali a yankin Gabas taTsakiya ya bayyana a sarari

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Amurkawa sun ba wa sojojin saman gwamnatin yahudawan sahayoniyya damar amfani da sansanonin sojinsu na sama, da kayayyakin kariya da suka aike musu, da ake daukan hakan a matsayin wani nau’i na shiga cikin ayyukan wuce gona da iri da suke faruwa a halin yanzu a yankin, don haka ana da imanin Amurka ta yi tarayya da gwamnatin yahudawan sahayoniyya a fagen kunna wutar tashe-tashen hankalin da ke faruwa a yanzu karara.

Abbas Araqchi ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin, inda ya bayyana cewa; Har zuwa yanzu haka suna ta samun sakonni daga kasashe daban-daban na duniya, da kuma bayanai da dama da aka fitar, wadanda suka hada da tofin Allah tsine, kan harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran a yankin Gabas ta Tsakiya da duniya.

Araqchi ya kara da cewa: Kasashen Japan, Indonesia, Malaysia, da dukkanin kasashen yankin da ma wasu kasashen Turai sun yi Allah wadai da ayyukan ta’addancin yahudawan sahayoniyya, yana mai cewa: Matsayin tofin Allah tsine ga wannan wuce gona da iri da ‘yan sahayoniyya suka yi al’amari ne mai girma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments