Amir Abdallahiyan ministan harkokin wajen kasa iran ya aikeda sakonni mabanbanta ga takwararonsa na kasashen Azarbaikan, Uzbakistan ,Afghanistan, Pakistan, Tajikisan,Turkmenistan Turkiya, Iraki, Krygystan ,Kazakhstan da kuma Indiya na murnar shiga sabuwar shekara hijira shamsiya da bikin Eidin Norooz.
A jiya laraba 20ga watan maris ne aka fara bukukuwan shiga sabuwar shekara wato shekara ta 1403 hijita shamsiya a kasar iran da ma sauran kasashen makwabta da suka kada alaadu iri daya, ya fadi a sakon taya murnar cewa Eidin Nowroz Edi ne na alada da tsohuwar wayewa da aka gada a tsawon shekaru dubbai da suka gabata da ya zama wani abu da kasashen suka yi tarayya akai
Haka zalika ya nuna cewa Alummar iran da gwamnati iran suna damuwa matuka da manufofin siyasar da suka shafi makwabtaka da juna domin zurfafa zumunci da hadin gwiwa don cin gajiyar juna, Ya bayyana fatan cewa, za a bi hanyar, sakamakon muradun kasashe da shugabannin kasashen yankin, da kuma shirya fage na ci gaba, da wadata, da tsaron yankin.