MDD: Yunwa Da Cuttuka Ne Zasu Fi Kashe Mutanen Gaza Nan Gaba

Kwamishinan hukumar UNRWA mai kula da al-amuran bada agaji a kasar Falasdinu da aka mamaye, ya bayyana cewa nan gaba kadin yunwa da kuma cututtuka

Kwamishinan hukumar UNRWA mai kula da al-amuran bada agaji a kasar Falasdinu da aka mamaye, ya bayyana cewa nan gaba kadin yunwa da kuma cututtuka ne zasu fi kissan falasdinawa a Gaza fiye da makaman HKI.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Philippe Lazzarini, babban jami’i mai kula da hukumar UNRWA yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa yunwa da cututtuka ne zasu fi kashe Falasdinawa a Gaza idan kasashen duniya sun ki tsaida yakin da HKI take kaiwa kan yankin.

Ya ce wannan musiba ta kofar ragon wanda HKI ta samar ba ta dabi’a bace, ko kuma wanda HKI ta samar zai kasance mafi kisa ga falasdinwa a Gaza nan gaba.

Lazzarini ya ce za’a kaucewa wannan musibar ne kawai idan an cika yankin Gaza da abinci asasheshe. shugaban UNRWA ya kara da cewa lokaci yayi da kasashen duniya zasu dauki matakin da suka dashe kafin lokaci ya kure masu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments