MDD Ta Yi Allah Wadai Da Ayyukan Isra’ila Masu Kwatankwacin Manyan Laifukan A  Gaza

Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kara tabarbarewar al’amura a Gaza, yana mai bayyana cin zarafin da Isra’ila ke yi

Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kara tabarbarewar al’amura a Gaza, yana mai bayyana cin zarafin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a matsayin “ayyukan da ke kama da manyan laifukan kasa da kasa.”

Joyce Msuya, shugabar rikon kwarya ta hukumar jin kai ta OCHA, ta bayyana hakan a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu ranar Talata.

“Muna ganin ayyukan da suka yi kama da manyan laifuka na kasa da kasa,” in ji ta.

Ta yi Allah wadai da farmakin da sojojin Isra’ila suka yi a baya-bayan nan a arewacin Gaza, inda ta yi nuni da cewa an kori fararen hula daga gidajensu.

Ta bukaci kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su yi amfani da matsin lamba na diflomasiyya da na tattalin arziki don hana ci gaba da wahalhalun na al’ummar Falasdinu.

Kungiyoyi takwas da suka hada da Oxfam da Save The Children sun ce: “A halin yanzu halin jin kai a Gaza ya kai kololuwa tun lokacin da aka fara yakin a watan Oktoban 2023.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments