Babbar jami’ar Majalisar Dinkin Dinkin kan hakkokin bil adama Francesca Albanese ta kwatanta zirin Gaza da “sansanin gudun hijira mafi girma kuma abin kunya ga duniya a ƙarni na 21,” kamar yadda ta wallafa a shafinta na X, inda ta tabbatar da cewa Isra’ila na aikata kisan kiyashi a kan unguwanni da asibitoci da makarantu da sansanonin gudun hijira da mafaka duk a lokaci guda.
Zargin na Albanese na zuwa ne bayan wani hari da aka kai a ranar Asabar inda Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 ta kuma jikkata da dama a wani hari da ta kai wata makaranta a Birnin Gaza
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa WAFA ya ce tankokin yaƙin Isra’ila sun yi luguden wuta kan makarantar, wacce ta zama mafaka ga Falasɗinawan da suka rasa gidajensu.
“An yi wa fiye da mutum 40 shahada an jikkata da dama bayan harin na Isra’ila a makarantar Al-Tabai’een a yankin Al-Sahaba a Birnin Gaza,” kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan yankin Mahmoud Basal ya wallafa tun da farko a saƙon da ya wallafa a Telegram.