Mayakan Kungiyar Hizbullah Sun Kai Hare-Hare Kan Biranen Tel Aviv Da Haifa A Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi luguden makamai masu linzami kan biranen Tel Aviv da Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi luguden makamai masu linzami kan biranen Tel Aviv da Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila

Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar da cewa: An yi ta jin karar gargadi a birnin Tel Aviv da wasu garuruwa da dama na haramtacciyar kasar Isra’ila kan yahudawan sahayoniyya su gudu zuwa  maboyar karkashin kasa, sakamakon hare-haren makamai masu linzami da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Labanon ta kaddamar kan yahudawan sahayoniyya.

Kafofin yada labaran sun kuma watsa rahoton cewa: An samu katsewar wutar lantarki a wasu yankuna na birnin Tel Aviv, bayan hare-haren makaman masu linzami da kungiyar Hizbullah ta kai.

Kamar yadda wasu kjafofin watsa labarai suka wallafa faifan bidiyo da ke nuna faduwar makamai masu linzamin kai tsaye da kuma barkewar wuta a matsugunin Ramat Gan da ke Tel Aviv.

An bayyana cewa hukumomin yahudawan sahayoniyya sun yanke shawarar rufe filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke Tel Aviv sakamakon hare-haren kan birnin Tel Aviv.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments