Matasan Belgium: Muna Alfahri Da Kai Kan Yadda Ka Damu Da Al-ummar Falasdinu

Gungun matasa a kasar Belgium sun rubutawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae wasika, don mayar masa da amsa kan wasikarsa garesu

Gungun matasa a kasar Belgium sun rubutawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae wasika, don mayar masa da amsa kan wasikarsa garesu bayan fara yakin Tufanul Aksa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto wasikar tana cewa “muna alfakhari da yadda kake kokarin tabbatar da adalci, da kuma gaskiya.  Har’ila da kuma yadda ka jajirce wajen taimakawa al-ummar Falasdinu wacce ake zalunta da kuma taimakawa raunana a duniya.

Kafin haka dai jagoran juyin juya halin musulunci ya rubutawa matasan kasashen yamma wadanda suka hada da kasashen Turai da Amurka wasika, inda ya bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa ta hanyar zanga zangar neman a dakatar da yaki a Gaza, a kuma yentar da kasar Falasdinu daga HKI.

Jagoran ya fadawa matasan kan cewa matsayin da suka dauka na neman dakatar da yaki a gaza, matsayi ne wanda ya dace a tarihin duniya da kuma wannan zamanin.

Matasa daga kasar Belgiun ne suka rubuta wannan wasikar suke kuma godewa jagoran da irin jagorancin da yake bayarwa don tabbatar da zaman lafiya a duniya da kuma musamman kubutar da al-ummar Falasdinu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma wadanda suke amfani da ita don ci gaba da mulkin mallaka a kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments