Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Ce Suna Kokarin Ganin An Cimma Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Da Lebanon

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya ce: Jamhuriyar Musulunci tana ci gaba da kokarin ganin an cimma bukatar dakatar da bude wuta a Falasdinu

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya ce: Jamhuriyar Musulunci tana ci gaba da kokarin ganin an cimma bukatar dakatar da bude wuta a Falasdinu da Lebanon

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Arif ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da kokarin neman an cimma yarjejeniyar dakatar da yakin, da aikewa da agajin jin kai ga mutanen da suka rasa matsugunansu, da kuma samar da tsagaita bude wuta a Falastinu da Lebanon.

Kafin tafiyar zuwa birnin Riyadh na Saudiyya a safiyar yau Litinin domin halartar taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Riza Arif ya bayyana cewa: Za a gudanar da wannan taro ne bisa shawarar Iran, yana mai bayyana cewa; Makasudin wannan taro shi ne kawo karshen yaki da zubar da jini a Lebanon da Falastinu.

Mataimakin shugaban kasar na farko ya bayyana fatansa na ganin cewa: Zaman taron ya kai ga samun sakamako mai kyau a wannan taro tare da shawarwarin da suka dace daga kasashen da suke halartar taron, da kuma samun nasarori masu ma’ana ta fuskar bayar da taimako ga ‘yan gudun hijira da wadanda hare-hare da laifuffukan yahudawan sahayoniyya suka shafa, wanda ke nuni da cewa a cikin wannan yanayi za a shiga mataki na uku na cewa, manufar Iran da dukkanin kasashen musulmi da na Larabawa ita ce cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta dindindin a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments