Masu Hakar Ma’adinai 13 Sun Rasu Bayan Ruftawar Kasa A Filato Najeriya

Akalla matasa 13 ne ake fargabar sun mutu bayan ruftawar kasa a wurin hakar ma’adinai a Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato. Aminiya ta

Akalla matasa 13 ne ake fargabar sun mutu bayan ruftawar kasa a wurin hakar ma’adinai a Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.

Aminiya ta lura cewa yawancin masu hakar ma’adinan da suka rasu matasa ne masu shekaru 18 zuwa 30.

Shugaban karamar hukumar, Dokta Joshua Riti, ya ce mutum bakwai daga cikin mamatan ’yan asalin karamar hukumar ne.

Ya bayana cewa wurin hakar ma’adinan da abin ya faru, ya yana kan iyakan kananan hukumomin Bassa, Jos ta Kudu da kuma Jos ta Arewa.

“Wannan abin takaici ne, matasa suna neman abin dogaro da kansu irin wannn ya rutsa da su.

“Sun fita suna aikin karfi domin rufa wa kansu asiri a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki, amma suka gamu da ajalins,” in ji Dokta Riti.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments