Masar Ta Jaddada Yin Watsi Da Shirin Yahudawan Sahayoniyya Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira

Masar ta yi gargaɗi game da shirye-shiryen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na neman tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Gaza Majiya gwamnatin Masar ta sake

Masar ta yi gargaɗi game da shirye-shiryen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na neman tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Gaza

Majiya gwamnatin Masar ta sake sabunta kakkausar murya da Masar ta yi na kin amincewa da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza yin gudun hijira zuwa birnin Sinai na Masar, tana mai jaddada cewa: Masar ba za ta amince da cimma muradun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan Falasdinawa ba.

Majiyar Masar ta tabbatar da cewa: Kalaman da wasu jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi na cewa matsalar ita ce Masar din ba ta barin mazauna Gaza shiga cikin kasarta, majiyar ta tabbatar da anniya da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na mayar da Falasdinawa zuwa birnin Sinai na Masar, wanda kasar ta Masar ta yi watsi da shi kwata-kwata. Kamar yadda majiyar Falasdinawa ta Sama ta bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments