Mali Ta Jadadda Ci Gaba Da Karfafa Alaka Da Iran

Wata tawagar manyan jami’an kasar Mali, ta gana da shugaban rikon kwarya na kasar Iran, Mohammad Mokhber, inda ta mika sakon ta’aziyya ga Iran sakamakon

Wata tawagar manyan jami’an kasar Mali, ta gana da shugaban rikon kwarya na kasar Iran, Mohammad Mokhber, inda ta mika sakon ta’aziyya ga Iran sakamakon rasuwar shugaban kasar Ibrahim Ra’isi da wasu mukarabansa ciki harda ministan harkokin wajen kasar.

Yayin ganawar Shugaban Dr Mohammad Mokhber ya mika godiyarsa ga gwamnati da al’ummar kasar Mali bisa nuna juyayi da goyon bayansu ga gwamnati da al’ummar kasar Iran.

Shugaban riko na kasar ta Iran, ya bayyana wajabcin yin amfani da damar da suke da ita wajen kyautata huldar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Ya kuma bayyana cewa, “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana tare da ‘yan’uwanta na kasar Mali kuma a shirye take wajen musayar kwarewa domin cin moriyar juna”.

A nasa bangare wanda ya jagoranci tawagar kasar ta Mali a Tehran, ya bayyana jimaminsa da kuma goyon bayan shugaban gwamnatin rikon kwarya da al’ummar kasarsa ga al’ummar Iran.

A yayin da yake yi wa Dr Mokhber fatan samun nasara a wannan sabon mukamin nasa, ya yi nuni da muradin kasarsa da kuma burinsa na fadada hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da fadada hadin gwiwa kamar yadda ya kamata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments