Makarantan Alkur’ani Na Kasar Iran Suna Samun Matsayi A Gasar Da Ake Yi A Kasar Kuwait

Makarantan alkur’ani mai girma na kasar Iran da suke halartar gasar da ake yi a kasar Kuwaiti suna samun matsayi da kuma yabo daga al’ummar

Makarantan alkur’ani mai girma na kasar Iran da suke halartar gasar da ake yi a kasar Kuwaiti suna samun matsayi da kuma yabo daga al’ummar kasar ta Kuwaiti.

Jakadan Jamhuriyar Musulunci a kasar Kuwaiti ya rubuta a shafinsa na X cewa:  Makarantan kur’ani Iraniyawa sun ja hankalin al’ummar kasar Kuwaiti ta hanyar kyautata karanta littafin Allah, suna yin tarayya a gasar da ake yi a Kuwaiti wacce ita ce karo na 13. Daga cikin mahalarta zaman gasar da akwai ministan harkokin addini Muhammad al-Wasmi da kuma jakadan Iran a Kuwaiti  Muhammad Tutunchi.

Da akwai mahardatan kur’ani su 127 da suke halartar gasar daga kasashe 75,kuma suna yin tarayya matakai daban-daban na karatun littafin Allah mai tsarki.

Daga jamhuriyar musulunci ta Iran da akwai mahardata da su ka hada Muhamamd Ridha Zahiri, da Habib Sadakat,sai kuma Muhammad Husain Malaki Najad.

A gefe daya kuma an gudanar da baje koli na kur’ani mai girma wanda ya hada baje rubuce-rubuce na kur’ani masu tsawon tarihi ko kuma wadanda aka kyautata rubutunsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments