Makamai Masu Linzami Masu Sarrafa Kansu Na Hizbullah,Sun Tarwatsa Sojojin HKI A Kudancin Lebanon

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun tarwatsa gungun sojojin HKI tare da tankunan yaki samfurin mirkava a lokacinda suka shiga wasu yankuna a cikin

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun tarwatsa gungun sojojin HKI tare da tankunan yaki samfurin mirkava a lokacinda suka shiga wasu yankuna a cikin kudancin kasar Lebanon.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa dakarun Hizbullah sun yi amfani da makamai masu linzami wadanda kuma suke sarrafa kansu, kan sojojin yahudawa wadanda suka shiga kasar daga kudancin kasar har zuwa garin Aita al-Shaab, inda suka wargaza tankunan yaki guda 3 sannan suka halaka sojojin yahudawan da dama, wasu kuma suka ji rauni.

Tun bayan shahadar Sayyis Shahid Hassan Nasarallah shugaban kungiyar Hizbullah ne, sojojin HKI suke kokarin shiga da kuma mamaye kasar Lebanon daga kudancin kasar amma sun kasa yin hakan har yanzu.

A cikin watan octoban shekara ta 2023 ne kungiyar take amfani da wadannan makamai don wargaza tankunan yakin na HKI. Hizbullah ta shiga yaki da HKI ne a ranar 8 ga watan Octoba na shekara ta 2023 don tallafawa mutanen Gaza, wadanda yahudawan sukewa kissan kiyashi. Ya zuwa yanzu sun kashe Falasdinawa kimani 42. Sannan wasu kimani dubu 100 suka ji rauini.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments