Majalisar dokokin kasar Pakistan ta amince da guduri wanda yayi allawadai da HKI kan kissan da ta yiwa shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a masaukinsa dake nan birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar kafafen yada labaran kasar Pakistan na fadar haka a jiya Jumma’a. Sannan dukkan yan majalisar sun amince da dokar wacce ta yi allawadai da HKI. Kudurin har’ila yau ya yi allawadai da ayyukan ta’addancin HKI na kissan Haniya. Banda haka kudurin ya bayyana cikken goyon baya ga al-ummar Falasdinu da ake zalunta.
Daga karshe kudurin ya bukaci a tsagaita bude wuta a gaza a kuma kawo karshen kisan kiyashin da akewa al-ummar Falasdinu a gaza da sauran yankunansu da aka mamaye.