Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah Wadai Da Kai Hari Kan Rundunarta Ta UNIFIL

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan rundunar tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta UNIFIL a matsayin laifin

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan rundunar tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta UNIFIL a matsayin laifin yaki

Majiyar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan rundunar tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta UNIFIL da ke kudancin kasar Lebanon a matsayin laifin yaki.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa: Duk wani hari da aka kai kan rundunar tsaron UNIFIL a kudancin kasar Lebanon yana iya zama laifin yaki, yana mai jaddada cewa bai kamata a kai musu hari ta kowace hanya ba.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric, ya ce har yanzu dakarun wanzar da zaman lafiya na UNIFIL suna nan a matsayinsu, kuma kai musu hari ya zama saba wa dokokin kasa da kasa.

Kasar Spain ta kuma yi Allah wadai da kalaman fira ministan mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu game da rundunar UNIFIL, yana mai jaddada cewa: Rundunar ta UNIFIL ba za su bar wuraren da suke a kudancin Lebanon ba. Haka kuma ta yi kira da a dakatar da jigilar makamai zuwa ga ‘yan mamaya da suke aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments