Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce: Zirin Gaza Na Cikin Mummunan Yanayi A Halin Yanzu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Zirin Gaza na cikin wani mummunan yanayi ta fuskar cututtuka, kashe-kashen rayukia, raunuka da hasarar rayuka Babbar jami’ar kula da

Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Zirin Gaza na cikin wani mummunan yanayi ta fuskar cututtuka, kashe-kashen rayukia, raunuka da hasarar rayuka

Babbar jami’ar kula da ayyukan jin kai da sake gina yankin Zirin Gaza, Sigrid Kaag ta bayyana cewa: Zirin Gaza ya kai wani sabon mataki mai ban tsoro da muni dangane da raɗaɗi, barna, rauni da hasarar rayukan bil’Adama.

Madam Kaag ta kara da cewa: A duk lokacin da ta je Gaza, ta kan kasa yin tunani sauwara irin barnar da take gani da idonta. Tana mai yin nuni da ire-iren cututtukan da suke yaduwa ayankin saboda rashin tsafta musamman a lokacin zafi.

Kaag ta kuma jaddada cewa: Dukkan ma’aikatan agaji a Gaza suna fuskantar irin wannan matsala da al’ummar yankin suke fuskanta.

Sannan Madam Kaag ta jaddada cewa: Dole ne a kiyaye dokokin kasa da kasa, tare da samar da damar shiga yankin cikin aminci domin ma’aikatan jin kai su samu yancingudanar da taimako da ayyukan jin kai na bil’Adama musamman ga mata da kananan yara gami da tsofaffi ciki har da rarraba ruwa mai tsafta da kayayyakin tsafta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments