Mahajjatan Bana Suna Ci Gaba Da Gudanar Da Ayyukan Hajji A Ranar Lahiya A Mina

Mahajjata aikin hajjin bana sun nufi Mina domin gudanar da jifan shaida a Jamarat Mahajjatan bana da suka ziyarci dakin Allah sun fara isowa Mina

Mahajjata aikin hajjin bana sun nufi Mina domin gudanar da jifan shaida a Jamarat

Mahajjatan bana da suka ziyarci dakin Allah sun fara isowa Mina da asubahin yau Lahadi, domin jifan Jamarat al-Aqaba da yankan layya, a ranar farko ta Idin Al-Adha mai albarka, sannan sauran ayyukan wannan rana da suka hada da aski ko saisaye, sannan dawafi da sa’ayi tsakanin Safa da Marwah. Bayan haka alhazai sun ci gaba da kammala ibadarsu, zasu zauna a Mina natsawon kwanakin tashriq, suna yawaita ambaton Allah da gode masa, sannan suka kammala jifan Jamarat guda uku.

Mahukuntan Saudiyya sun sanar da cewa: Adadin maniyyatan bana ya kai miliyan 1,833,164, wadanda suka hada da mahajjata 1,611,310 da suka fito daga kasashe sama da 200, ta hanyar tashar jiragen ruwa daban-daban, da kuma mahajjata 221,854 daga ‘yan kasar da mazauna yankin, lamarin da ya nuna cewa adadin maza daga cikin jimillar ya kai. 958,137, da kuma alhazai mata da suka kai dubu 875 da 27.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments