Maduro ya lashe zaben shugaban kasar Venezuela a wa’adi na uku

An sake zaben Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasar Venezuela domin yin wani sabon wa’adin shugabanci karo na uku, kamar yadda hukumar zaben kasar ta

An sake zaben Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasar Venezuela domin yin wani sabon wa’adin shugabanci karo na uku, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Elvis Amoroso, shugaban hukumar zabe ta CNE, ya ce Maduro mai shekaru 61, ya samu kashi 51.2 cikin dari na kuri’un da aka kada jiya Lahadi, wanda ya tabbatar masa da wani sabon wa’adin mulki na uku na tsawon shekaru shida.

Amoroso ya shaidawa manema labarai cewa dan takarar adawa Edmundo Gonzalez Urrutia ya samu kashi 44.2 na kuri’un da aka kada.

A halin da ake ciki, Maduro ya yabawa masu sa ido kan zaben sama da 900 da suka sanya ido a kan yadda aka gudanar da zaben, ya kuma yi tir da wadanda ke zargin an yi magudi a zabe, yana mai cewa, “Mun sha ganin irin wannan a baya.”

Maduro, tsohon direban bas wanda ya zama shugaban kasa bayan mutuwar ubangidansa Hugo Chavez a shekarar 2013, an sake zabensa a shekara ta 2018 duk da adawar da Amurka ta nuna kan hakan.

Tun daga watan Nuwamban shekarar 2019, takunkumin da Amurka ke kakaba wa kasar,  ya sanya hauhawar farashin kayayyaki a Venezuela ya kai sama da kashi 4,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments