Maduro: Netanyahu Wani Dodo Ne Masha Jini Da Turai Da Amurka Su Ka Samar Da Shi

Shugaban kasar Venezuela  Nicolas Maduro ya bayyana Fira Ministan HKI da cewa, wani Dodo ne masha-jini wanda kasashen turai da Amurka su ka samar da

Shugaban kasar Venezuela  Nicolas Maduro ya bayyana Fira Ministan HKI da cewa, wani Dodo ne masha-jini wanda kasashen turai da Amurka su ka samar da shi, tare da cewa; Abinda yake yi, ko Hitler ba shi da tsaurin zuciyar aikatawa.

Shugaban kasar ta Venezuela ya kara da cewa, abinda Fira ministan Isra’ila yake yi a Falasdinu da Lebanon , kisan kiyashi ne ba yaki ba.

Maduro ya kuma ce: “Netenyahu yana kai wa asibitoci, makarantu da masallatai hare-hare a Gaza, haka nan kuma sansanonin ‘yan gudun hijira, ya za a kira wannan yaki? Abinda yake faruwa kisan kiyashi ne.”

Nicholas Maduro ya bayyana mamakinsa akan yadda Netenyahu yake da rashin ta ido da har zai bai wa MDD umarnin ta janye sojojinta na zaman lafiya daga kudancin Lebanon.

Shugaba  Maduro  wanda ya gabatar da jawabi domin tunawa da zagayowar cikar shekara daya na yakin Gaza, ya kara da cewa; Abinda yake faruwa a gabas ta tsakiya ba rikici ba ne,wata manufa ce ta mulkin mallakar Amurka, Birtaniya da turai da suke son shimfida ikonssu a wannan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments