Limamin Juma’a: Shahid Sayyid Nasrallah Jagoran Gwgawarmaya Ne Da Kuma Hadin Kan Lebanon

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran a yau, ya bayyana Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a matsayin wanda yake dauke da tutar daukaka a

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran a yau, ya bayyana Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a matsayin wanda yake dauke da tutar daukaka a duniyar larabawa, haka nan kuma ramzi ne na hadin kai a cikin kasar Lebanon.

Hujjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi Fard ya kuma bayyana shahid Hassan Nasrallah da cewa ya kasance ma’abocin jarunta da kuma hikima.

Limamin na Tehran ya kuma yi ishara da yadda shahid Sayyid Hassan Nasrallah ya share gomiya uku yana jagorantar kungiyar ta Jihadi da kuma yi wa mutane tarbiyya ta addini da kyawawan halaye da siyasa a karkashin koyarwar alkur’ani mai girma da Ahlul bayt (a.s).

Hujjatul Islam Hassan Abu Turabi Fard ya kuma bayyana Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da cewa, babban mataimaki ne na jagoran juyin juya halin musulunci na Iran a duniyar musulunci, kuma rawar da yake takawa, yanzu babu wanda zai iya cike wannan gurbin nashi.

Limamin na Tehran ya kuma bayyana cewa; Sahidai irin su Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, Isma’ila Haniyyah, Yahya Sinwar, Nilofurushan da wasunsu, suna a matsayin ramzi ne na tsayin daka, masu neman gaskiya da son shimfida adalci a doron kasa da kare hakkokin wadanda ake zalunta.

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments