Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Juma’a A Birnin Tehran Ya Ce Harin Yemen KanTel-Aviv Gargadi ne

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya yi magana kan harin da Yemen ta kai a kan birnin Tel Aviv na haramtacciyar

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya yi magana kan harin da Yemen ta kai a kan birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila

Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran Hujjatul-Islam Sayyid Muhammad Hasan Abu-Turabi Fard ya bayyana cewa: Harin da jiragen saman yakin Yemen suka kai birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila, hari ne ‘yan gwagwarmaya suka kai tsakiyar birnin yahudawan sahayoniyya TelAviv, kuma kusa da ofishin jakadancin Amurka, wani karin gargadi ne ga kawo karshen zaluncin yahudawan  Sahayoniyya kan al’ummar Gaza.

Haka nan Hujjatul-Islam Sayyid Muhammad Hassan Abu Turabi Fard ya jaddada cewa: Harin ‘yan gwagwarmayar Yemen suka kai da jirage marasa matuka ciki kan birnin Tel Aviv a safiyar yau Juma’a, jiragen sama ne da matasan Yemen suka kera da kansu

Yana mai jaddada cewa: Matsayin al’ummar Gaza ya sake haifar da wani suna ga al’ummar musulmi, ya kuma kara da cewa: Tsohon fira ministan yahudawan sahayoniyya ya ce: A kullum ana kashe sojojin su a Gaza kuma gwamnatinsu ta karye tare da durkushewa kuma a halin yanzu ba ta da wani tasiri ko kima a idon yahudawa. Haka nan babban hafsan sojin yahudawan sahayoniyya mai murabus ya ce: An yi galaba a kan sojojin yahudawan sahayoniyya a yakin Gaza, kuma yahudawa suna fama da rashin kayan aiki, rashin dabarun yaki, karancin abinci da abubuwan bukatun yau da kullum.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments