Rahotanni sun tabbatar da cewa, jiragen yakin Isra’ila sun keta hurumin sararin samaniyar birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon, a daidai lokacin da gwamnatin Haratacciyar kasar Isra’ila ke barazanar kaddamar da wani mataki na soji a kan kasar ta Lebanon.
Jiragen yakin na Isra’ila sun yi shawagi cikin sararin samaniyar birnin Beirut ne da sanyin safiyar yau Lahadi, kamar yadda tashar Resistance News Network, ta ruwaito a dandalinta na telegram.
Rahoton ya ce an ga jiragen yakin sun keta hurumin sararin samaniyar birnin suna shahawagi a sama.
Haratacciyar kasar Isra’ila ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Labanon bayan fara yakin kisan kiyashin a zirin Gaza, wanda ya fara tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya yi sanadiyar mayar da martani daga bangaren dakarun Hizbullah na kasar Lebanon.
Kungiyar dai ta dauki matakin mayar da martani kan harin ne ta hanyar harba daruruwan rokoki a yankunan arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye.
Tel Aviv dai na ci gaba da yin barazanar mayar da Lebanon kamar yadda ta mayar da Gaza.
A farkon watan nan ne dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ta amince da shirin kai wa kasar Lebanon hari, lamarin da ke kara nuna fargabar cewa gwamnatin Haratacciyar kasar Isra’ila na iya shiga cikin yaki da Lebanon a kowane lokaci.
Sai dai babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar yayin da yake magana kan barazanar da Isra’ila ke yi da cewa “idan har aka shiga yaki na bai daya a kan kasar Labanon, to kuwa tabbas ‘yan gwagwarmaya zasu yi yaki babu kakkautawa, kums ba tare da ka’ida ko kiyaye wata iyaka ba.