Lebanon: Jakadun Kasashen Waje Sun Ziyarci Tashar Jiragen Sama RHIA Don Gano Kariyar Jaridar Telegaram

Ministan sufuri na kasar Lebanon Ali Hamieh ya jagoranci tawagar jakadun kasashen waje da suke kasar Lebanon da kuma yan jaridu zuwa cikin sassa daban

Ministan sufuri na kasar Lebanon Ali Hamieh ya jagoranci tawagar jakadun kasashen waje da suke kasar Lebanon da kuma yan jaridu zuwa cikin sassa daban daban na tashar jiragen sama na Rafikul Hariri Int. Airport da ke birnin Bairut don tabbatar masu kariyar wata jarida ta kasashen yamma wacce take zargin kungiyar Hizbullah da ajiye makamai a cikin tashar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ali Hamieh ministan sufuri na kasar Lebanon yana cewa: duk tare da keta hurumin sararin samaniyar kasashen Lebanon wanda jiragen yakin HKI suke yi tun da dadewa hukumomi a tashar jiragen RHIA sun yi kokarin ganin suna yin abinda ya dace don tabbatar da cewa tashar jiragen saman yana aiki.

Daga cikin jakadunan kasashen wajen da suka sami ziyarar ganewa idanu a sassa daban daban na tashar jiragen saman dai akwai jakadun kasashen Tarayyar Turai, Jamaus Indiya, Masar Pakistan, China, Brazil, Ivory Coast, Morocco, da kuma Jordan.

Jakadan kasar Masar , Alaa Moussa yace wannan ziyarar ganin ido ya tabbatar da goyon bayan da kasar Masar take bawa kasar Lebanon, sannan ya kara da cewa dakatar da yaki a Gaza ce kawai zai dutse watan yajin da ya game wasu sassa nag abas ta tsakiya.

Sai kuma shugaban tashar jiragen saman na RHIA Fadi al-Hassan ya kara jaddada cewa tashar jiragen saman tana kula da dukkan dokokin kasa da kasa na kula da tashoshin jiragen sama.

Kafin haka dai Jaridar Telegram ta kasar Burtania ta yi wani rubutu wanda ya ke zargin kungiyar Hizbullah da ajiye makamai a tashar jiragen saman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments