Mayakan kungiyar Hizbullah na kasar lebanon sun kai hare hare kan sansanin sojojin HKI a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Litinin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayanin da kungiyar ta fitar a jiya Litini, inda a cikinsa ta ce ta yi amfani da makaman attilari a luguden wutan da ta yi a kan sansanin sojojin HKI da ke ‘Limon da ke arewacin garin Jalil a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.
Kungiyar dai ta shiga yaki da sojojin HKI ne tun cikin watan Octoban da ya gabata saboda tallafawa Falasdinawa wadanda suka shiga fafatawa da sojojin yahudawan Sahyoniyya a ranar 7 ga watan Octoba. Kuma ta kara da cewa zata ci gaba da kai hare hare kan sojojin HKI a matsugunansu da ke araewacin Falasdinu da suka mamaye har zuwa lokacinda zasu kawo karshen yaki a gaza.
Daubban daruruwan yahudawa yan share wuri zauna da suke arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye dai sun kauracewa yankin tun lokacin da kungiyar ta fara musayar wuta da sojojin HKI a arewacin falasdini da kuma kudancin kasar Lebanon.