Kungiyoyin Falasdinawa sun yi tir da allawadai da hare haren jiragen yakin HKI kan karamin ofishin jakadancin JMI da ke birnin Damascus na kasar Siriya a ranar Litinin. Sun kuma kara da cewa, wadannan hare haren sun nuna gazawar HKI na kaiwa ga manufofinta a yankin da take fafatawa da kungiyoyin Falasdinawa a zirin Gaza da kuma magoya bayansu a sauran kasashen yankin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar kungiyoyin falasdinawa suna cewa ayyukan ta’addanci wanda HKI ta yi a Gaza da Lebanon da siriya sun nuna cewa samuwar HKI ya girgiza, kuma akwai yiyuwan ta rushe, kuma kawancen masu gwagwarmaya a yankin suna samun nasara a kanta da kawayenta.
Daga karshe kungiyoyin sun bayyana cewa hare haren na Damascus hare hare kan dukkan kasashen Larabawa da kuma kasashen musulmi. Kuma yakamata a ladabatar da ita da wasu karin hare hare masu karfi.