Kungiyar kwadago a tarayyar Najeriya ta nuna takaicinta sannan tace gwamnatin tarayya ta yaudari shuwagabannin kungiyar a lokacinda suka amince da naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar ta NLC Joe Ajaero yana fadar haka a Abuja, ya kuma kara da cewa kungiyar ta amince da naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi ne tare da tsammanin ba za’a kara farashin man fiye da yadda yake ba. Amma sai kamfanin NNPC ta basu mamaki da sanarwan da ta bayar a jiya Talata.
Ajaero ya bukaci gwamnatin tarayyar ta maida farashin kamar yadda yake a da, ko kuma ta kara mafi karancin albashi zuwa 250,000
.
Sannan ta bukaci gwamnati ta saki dukkan wadanda aka kama a zanga zangar tsadar rayuwa da kuma mummunan shugabanci da aka yi a ranar 1 ga watan Augustan da ya gabata.