Kungiyar Kwadago a tarayyar Najeriya ta bukaci yansandan kasar su kawo karshen kissan masu zanga zanga su kuma saurari kiraye kirayensu na kawo karshen mummunar shugabanci.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto kungiyar Amnesty International na cewa jami’an yansanda sun kashe akalla mutane 13 a yayin zanga zangar matsalar rayuwa a kasar da aka fara a ranar 1 ga watan Augusta.
Labarin ya kara da cewa shugaban kungiyar kwadago Joe Ajaero yana cewa jami’an tsaron kasar basu yi abinda ya dace ba wajen fuskantar masu zanga zanga a kasar.
Mr Ajaero ya bayyana cewa a rahotannin da suka samu mutane fiye da 40 ne suka rasa rayukansu a wannan zanga zangar a cikin kwanaki biyu da suka gabata.
Ya kuma kara da cewa, daa yansandan sun yi ammafani da karfin da suka yi a kan masu zanga zanga a kan yan ta’adda, da tuna an kauda su a kasar nan.
Don haka ya kammala da cewa suna da labarin cewa yansanda sun yi amfani da karfi a jihohi da dama daga ciki har da Abuja daga ciki sun jefawa masu zanga zanga hayaki mai sa hawaye da kuma harbi da bindiga.
Amma jami’an yan sanda a kasar sun bayyana cewa mutane 7 ne kawai suka mutu ya zuwa yanzu saboda zanga zangar.