Kungiyar Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha  Ta Yi Allah Wadai Da Harin HKI Akan Iran

Sakataren kungiyar Larabawan yankin tekun Pasha Jasim al-badawi, ya bayyana cewa; Harin Da Isra’ila ta kai wa jamhuriyar musulunci ta Iran,abin yin tir da shi

Sakataren kungiyar Larabawan yankin tekun Pasha Jasim al-badawi, ya bayyana cewa; Harin Da Isra’ila ta kai wa jamhuriyar musulunci ta Iran,abin yin tir da shi ne da kuma takaici.

Jasim al-Badawi ya kuma kara cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Iran, keta hurumin kasar ne, sannan kuma yana cin karo da dokokin kasa da kasa, don haka kungiyar kasashen larabawa ta tekun Pasha tana yin tir da hakan.”

Sakataren kungiyar kasashen larabawan yankin tekun Pashan ya kuma yi kira da akai zuciya nesa tare da yin ishara da mummunan sakamakon da yake tare da yaki a cikin wannan yankin.

Haka nan kuma Badawi ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu domin rage rikici a cikin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments