Kungiyar kasashen Larabawa ta cire Hizbullah daga cikin wadanda take kira kungiyoyin ta’addanci

Kungiyar hadin kan Larabawa ta janye daga matsayinta na sanya kungiyar Hizbullah a matsayin “kungiyar ta’addanci”,  Hossam Zaki, mataimakin sakatare-janar na kungiyar Larabawa ya sanar

Kungiyar hadin kan Larabawa ta janye daga matsayinta na sanya kungiyar Hizbullah a matsayin “kungiyar ta’addanci”,  Hossam Zaki, mataimakin sakatare-janar na kungiyar Larabawa ya sanar da hakan.

Zaki ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka watsa ta tashar talabijin ta Al-Qahera ta Masar cewa,  “A cikin hukunce-hukuncen kasashen Larabawa da suka gabata, an sanya kungiyar Hizbullah a matsayin kungiyar ta’addanci.

A cewar babban jami’in, “kasashen mambobin kungiyar sun amince cewa, a janye kungiyar Hizbullah daga cikin kungiyoyi da ake kira na ta’addanci.

A nata bangaren, jaridar Al-Akhbar ta kasar Labanon ta nakalto majiyoyi na cewa, Zaki ya sanar da kungiyar Hizbullah cewa kungiyar Hadin kan kasashen Larabawa ta yanke shawarar janye matakin da ta dauka a baya kan Hizbullah da ke danganta kungiyar da ayyukan ta’addanci, kuma ta yi imanin cewa, Hizbullah tana da muhimmiyar rawa a makomar kasar  Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments