Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana aikata laifukan yaki a Gaza
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Yadda sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke amfani da tilastawa Falasdinawa yin kaura daga gidajensu da kuma wurga su cikin masifar yunwa a matsayin makamin yaki a Zirin Gaza ya kai matsayin laifukan yaki.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a jiya Juma’a ta bayyana cewa: Umarnin ficewar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila daga yankin Zirin Gaza ya hada da kashi 85% na yankin, kamar yadda sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka umarci mazauna arewacin Gaza 400,000 da su bar gidajensu tun farkon wannan wata na Oktoba da muke ciki.
Kungiyar ta ce sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da kara zafafa kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar yankin arewacin Gaza tare da hana kai kayan agajin jin kai misalin abinci da magunguna ga jama’ar da suka rage a yankin, lamarin da ya janyo ta’azzara matsalar jin kai. Kamar yadda sanarwar ta jaddada cewa: Sojojin mamaya sun tilasta wa Falasdinawa fararen hula barin arewacin Gaza ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da samar da mafaka ko kuma ba da tabbacin dawowar Falasdinawa a nan gaba ba.