Rahotanni da suke fitowa daga Lebanon sun amabci cewa mayakan kungiyar Hizbullah suna cigaba da dakile duk wani yunkuri na sojojin HKI da suke kokarin kutsawa cikin kasar, tare da kashe da kuma jikkata wasu daga cikinsu.
Sanarwar da kungiyar Hizbullah ta fitar ta kuma ce; Da safiyar yau sojojin HKI sun yi kokarin kutse ta hanyar garin Balida, sai dai mayakan na Hizbullah sun yi fada da su gaba da gaba tare da kashe wasu da dama daga cikinsu da kuma jikakata wasu.
A wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar dazu, ya bayyana cewa,za ta cigaba da jajurcewa wajen kare Lebanon, ba kuma za ta yi sassuci ba wajen taka masa birki.
Bugu da kari, bayanin ya zargi sojojin HKI da jefa bama-bamai masu kwafso da aka haramta amfani da su a duniya, tare kuma da zargin Amurka a matsayin mai goyon bayan dukkanin laifukan yakin da ‘yan sahayoniyar suke tafkawa.