Kungiyar Hamas Ta Yi Maraba Da Hukuncin Kotun Duniya Akan Mamayar HKI

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana jin dadinta akan hukuncin da kotun duniya ta yanke na; Rashin halarcin mamayar da Isra’ila take yi. Hamas

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana jin dadinta akan hukuncin da kotun duniya ta yanke na; Rashin halarcin mamayar da Isra’ila take yi.

Hamas ta ce;Wannan hukuncin da kotun ta yanke ya zama wani kalubale mai girma a gaban kungiyoyin kasa da kasa,tare da yin mira da a yi aiki da shi.

Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta bukaci ganin cewa; Babban zauren na MDD da kuma kwamitin tsaro sun yi aiki tukuru domin ganin an kawo karshen mamaya.

A jiya Juma’a ne dai kotun ta duniya ta yanke hukuncin cewa, mamayar HKI ba ta kan doka, tare kuma da gabatar wa babban zauren MDD wannan hukuncin nata.

Hukuncin kotun ya kuma bayyana matsugunan yahudawa ‘yan share wuri da ake ginawa da cewa suna cin karo da dokokin duniya.

Kusan watanni 10 da HKI take kai wa yankin Gaza hare-hare babu kakkautawa, wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan Falasdinawa dubu 38, da 848  tare da jikkata wani da ya kai dubu 89 da 459.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments