Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da zargin da gwamnatin Amurka ta yi na cewa; Gwamnatin ‘yan mamayar Isra’ila ta dauki matakin inganta yanayin jin kai a Gaza, kuma ta dauki furuci a matsayin wani tabbaci na cikakken hadin gwiwar gwamnatin Shugaba Biden a cikin mummunan yaki kan Gaza. kashe-kashen da ake yi wa al’ummar Falasdinu a Zirin na Gaza sama da shekara guda da kuma ayyukan kashe-kashen kare dangi da janyo masifar yunwa da aka ci gaba da yi a arewacin Zirin Gaza tsawon kwanaki talatin da biyar.
Kungiyar ta Hamas a cikin sanarwar da ta fitar a jiya Talata ta jaddada cewa: Da’awar da Amurka ta yi kan abin da ke faruwa a kasa ya tabata cewa karya ce, kuma rahotonnin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da na kasa da kasa wadanda suka tabbatar da cewa yankunan Zirin Gaza, musamman arewacin Gaza ya kai ga matakin bullar masifar yunwa, sakamakon bakar siyasar sojojin mamaya na kokarin wurga Falasdinawa cikin kanginmasifar yunwa, a daidai lokacin da suke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da ba su dauke da makamai.