Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ta Yi Maraba Da Matsayin Kotun Kasa Da Kasa Kan Falasdinu

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta O.I.C ta bayyana cewa: Kudirin Majalisar Dinkin Duniya yarjejeniya ce ta kasa da kasa kan adalci dangane da batun

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta O.I.C ta bayyana cewa: Kudirin Majalisar Dinkin Duniya yarjejeniya ce ta kasa da kasa kan adalci dangane da batun Falasdinu

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta yi maraba da amincewa da babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya ya yi da wani kuduri mai cike da tarihi da ke tabbatar da ra’ayin ba da shawara na kotun kasa da kasa kan rashin halarcin mamaye yankunan Falasdinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi, kuma kotun ta yin kira ga gwamnatin mamaya, da ta kawo karshen samuwarta a yankunan da kuma rusa dukkanin matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida daga yankunan da ta gudanar da gine-gine ba bisa ka’ida, a cikin tsawon watanni 12.

Kungiyar ta O.I.C a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Laraba ta bayyana cewa: Wannan shawarar ta bayyana matsayar kasa da kasa kan yin adalci ga al’ummar Falastinu da kuma cikakken goyon bayansu ga halalcin hakkokin al’ummar Falasdinu, gami da ‘yancin cin gashin kai da kuma tabbatar da zaman lafiya na kafa kasarsu mai cin gashin kanta a kan iyakokin da aka shata a ranar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967, tare da kasancewar birnin Al-Quds a matsayin fadar mulkin kasar ta Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments