Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta Popular Front ta yi watsi da kalaman ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan, inda ya bayyana goyon bayansu ga shirin neman jibge dakarun kasa da kasa a Zirin Gaza, bisa kudurin Majalisar Dinkin Duniya da nufin taimaka wa gwamnatin Falasdinu wajen gudanar da Mulki kan Yankin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta Popular Front ta ce, tana adawa da ire-iren wadannan kalamai, ta kuma jaddada cewa: Al’ummar Falastinu ce kadai da ke da ikon tantance makoma da kuma tsarin hukumar da ke mulki a Zirin Gaza.
Kuma ta kara da cewa: Duk wani yunkuri na neman jibge sojojin kasa da kasa a Gaza, ko da ta hanyar fitar da wani kuduri ne ko kuma ba tare da wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya ba, suna daukarsa a matsayin wani yunkuri na aiwatar da bukatar gwamnatin yahudawan sahayoniyya ko kuma wani sabon tsarin mamaya ne a yankin, lamarin da al’ummar Falastinu ba za su taba amincewa da shi ba a kowane irin yanayi.