Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi Dakarun kai daukin gaggawa da aikata cin zarafin bil-Adam a Sudan
Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Amnesty International ta zargi Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da kaddamar da hare-haren ramuwar gayya a jihar Al-Jazira da ke kudancin birnin Khartoum fadar mulkin kasar ta Sudan, wanda ya haifar da cin zarafi na kisan gilla da sace-sacen dukiyoyin jama’a da kuma kai wa mata hari.
Kungiyar kare hakkin bil-Adamar ta ce: Dakarun kai daukin gaggawa sun kuma kai hari kan garuruwa da dama a jihar Al-Jazira da ke gabashin kasar, inda suka kashe mutane a gidajensu da kasuwanni da kuma kan tituna, tare da wawashe dukiyoyi da suka hada da kasuwanni da asibitoci, kamar yadda ta ruwaito.
Sakamakon haka, Kungiyar ta Amnesty International ta bukaci dukkanin bangarorin da suke rikici da juna a Sudan da su kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan fararen hula, musamman bayan samun rahotannin kai hare-hare wuce gona da iri kan kauyuka akalla ashirin da biyar a shiyar gabashin jihar ta Aljezira.