Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 185

185-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wanda suka

185-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahida Murtadha Muttahari, ko kuma littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan mansu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma ciki  sirar Imam Al-Hassan Almujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku. Mun yi maganar wasu daga cikin ma’aikatan Mu’awiya dan Abusufyan, masu kekasheshen zuciya, wadanda suka hada da Samrata Dan Jundubin da kuma maigidan Ziyad dan Sumayya, har ila yau da kuma Busru dan Abu Arta’a, wadanda suka aikata ayyuka wadanda suka bakanta tarihin addinin musulunci bayan manzon Allah(s).

Mun bayyana cewa Busru dan Abu Arta’a ya je madina ya kashe duk wanda aka kawo masa kuma an tuhumeshi da hannu a kissan Khalifa Uthman. Sannan ya je Makka ya yi irin haka, sannan ya wuce zuwa kasar Yemen inda nan ma ya kashe mutane daga ciki har da yara kanana guda bitu na Abaidullahi dan Abbas, dan ammin manzon Allah (s), sannan ya kashe wani Bakinane wanda ya nuna rashin amincewarsa da kissan wadannan yara kanana.

Mun bayyana cewa kissan yaran Ubaidullahi, ya nuna irin kiyayya da Busru da maigindansa Mu’awiya suke kiyayya ga Banu Hashim  dangin manzon Allah (s). Bayan kissan wadannan yara kanana a Yemen wanda Busru yayi, wata mata ita ma daga banu kinana tana cewa ya kai wannan, ka kashe mazaje da wani dalili zaka kashe wadan nan yara, wallah a jahiliya da musulunci gaba daya ba’a kashesu. Ya kai dan Abi Arta’a duk sarautar da yake kashe yara da manya, babu rahama kuma babu sada zumunci mummunan sarauta ce.  

Malaman tarihi sun bayyana cewa Busru dan Abu Arta’a ya kashe mutene sun kai dubu 30, banda wadanda ya konasu da wuta.

Yanzun kuma sai ma’aikacin Mu’awiya na 4, wanda ya taimaka masa wajen tabbatar da ikonsa a kan musulmi. Wanda kuma shi ne Abuhuraira Addausi, an masa kunya da Abuhuraira ne saboda mege da yake wasa da ita a lokacinda yake karami. Saboda sonsa Mage, ya ruwaito hadisi daga manzon Allah (s) yana cewa, wata mata ta shiga wuta saboda magen da ta daureta bata bata abinci ba kuma bata barta da ci ciyayin kasa ba. Kamar yadda Bukhari ya ruwaito a cikin sahihinsa JZ na 2 SH 149.

A lokacinda hasken musulunci ya taso a Makka ya game kasashen larabawa Abuhuraira ya shiga musulunci kamar yadda mafi yawan Larabawa suka shiga. Ance ya musulunta a shekara ta 7 bayan hijira don haka shekara 2-3 ne kawai ya samu tare da manzon Allah (s).

Abuhuraira ya kasance cikin talauci a farkon rayuwarsa, ya dogara da roko kafin ya cika cikinsa. Idan bai samu ba yakan yi khidima wa mutane don cika cikinsa. Don haka yana daga cikin Ahlussuffa a Madina wadanda suke rayuwa da abinda wasu gidaje suka rage na abinci. Ko kuma idan manzon Allah (s) ya sami dukiya yakan basu.

Bayan manzon Allah (s) khalifa na biyu ya jawoshi kusa, ya kuma bashi walin Bahrain a shekara ta 21 sannan ya tube shi shekaru 2 bayan haka, wato a shekara 23 bayan hijira. Wannan kuma saboda ya ga yadda ya tara kudi. Ya ji labarin cewa Abuhuraira ya saye dawaki na dinari dubu da 600. Sai Abu huraira yace masa dabbobinsa ne suka yi ta haihuwa sannan kyauta da mutane suke bashi. Khalifa Umar yace masa, na sanya maka albashinka yadda zai isheka, don haka don abinda ka samu bayan haka kari ne kuma na musulmi ne.  

Sannan ya tashe ya daki Abuhuraira da bulalansa har ya ji masa ciwo a baya. Sannan ya ce amince ya dawo da duk abinda ya samu kari kan albashinsa. Daga nan sai Abu Huraira ya sake komawa kamar yadda yake.

Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacin Khalifa na uku Usman dan Affan wanda ya kusanto da shi, sannan yakan kirkoro hadisai na falalar Khalifa na uku ya jinginasu ga manzon Allah (s).

Ya ruwaito hadisi kan cewa manzon Allah (s) yace (Lalle ko wani annabi yana da badadi a cikin al’ummarsa, Kuma lalle badadina Usman ne ) kamar yadda Zahabi ya ruwaito a cikin Mizanul Itidal JZ 01 Sh 201.

A wani hadisin Abuhuraira yace manzon Allah (s) yace (Ko wani annabi yana da dan rakiya a al-janna, kuma dan rakiyata shi ne Uthman) Shima cikin Mizanul itidal JZ 3 Sh 32, hadisi na 5498.

Sai kuma bayan kisan Khalifa Uthman, sannan al-umma ta zabi Amirul muminina (a) Abuhuraira ya koma demesh wajen Mu’awiya dan abusufyan inda yace gaba da ruwaito masu hadisai na fafalar banu umayya, da kuma Mu’awiya dan abusufyan. Ya fadawa mutanen sham kan cewa, manzon Allah (s) yace: Lalle Allah ya amintar da mutane uku a kan wahayinsa, Ni da jibrilu, da Mu’awiya. A wani hadisin yace: Manzon Allah (s), ya bawa Mu’awiya wata kibiya, sai yace masa: Ka rike wannan kibiyar sai mun hadu a aljanna.

Da haka Abuhuraira yayi ta samun, kyaututuka daga banu umayya har zuwa shekarar Jama’a, inda ya je iraki tare da Mu’awiya. A lokacinda ya ga mutane da dama sun tarbeshi sai ya gurfana a kan guiwowinsa  ya yi ta dukan kansa sau da dama, sanni yace: (Ya ku mutanen Iraqi! Kuna tsammanin zai yi karya wa Allah da manzon Allah (s) ne?, kuma in kona kaina a wuta? Na rantse da Allah na ji manzon Allah (s) yana cewa: Lalle ko wani annabi yana da harami, luma lalle madina haramina ne, duk wanda ya haddasa fitina a cikinta, la’anar Allah da mala’iku da kuma mutane gaba daya su tabbata a kansa, kuma na shaida Aliyu (a) ya tada fitina a cikinta.)

A lokacinda labari ya kaiwa Mu’awiya dan Abusufyan dangane da abinda ya fada kan Aliyu (a) sai ya jawo shi kusa ya kuma sanya shi gwamnansa a madinan manzon Allah(s).

Da haka Abuhuraira ya sami daukaka a lokacin Banu Umayya, ya sami kudade ya gina bene a madina ya kuma auri mata wacce ya taba yi mata khidima don ya cika cikinsa a baya.

Sai dai a wajen yanuwammu Ahlussun shi ne rawiyatul Islam, ma’a a wajensa suka karbi hadisan addinin musulunci. Don cikin sahabban manzon Allah (s) ba wanda ya fi shi ruwaito hadisai daga wajensa. Abin mamaki shi ne, hadisi ya inganta kan cewa manzon Allah (s) yace: nine birnin ilmi Aliyu shi ne kofarsa, duk wanda yake son shiga birni ya bi ta kofarta). Kuma tarihin musulunci ya tabbatar mana cewa a cikin dukkan sahabban manzon Allah (s) babu wanda ya fi Aliyu dan Abitalib (a) ilmi. Kuma ya fi dukkan sahabban manzon Allah (s) dadewa a musulunci, ta yaya Abuhuraira ya fi shi yawan hadisai a wajen yanuwammu Ahlussunna? Shi ne ya ki ya bada ilmin ne (Allah ya kiyaye shi) ko kuma su suka ki karban ilminsa.

Amma na biyu ne, su suka ki karban ulmi daga wajensa, suka karbi hadisan Abuhuraine, wanda yake la’antarsa. Inna lillah wa inna ilaihi Raji’un.

A lokacin mulkin banu umayya wanda ya kai shekaru kimani 80,  sarakunansu daga Mu’awiya dan Abusufyan har zuwa na karshensu, basa binciken ma’aikatansu a wasu yankuna da daular musulunci, don tabbatar da cewa suna adalci suna kuma yin abinda ya dace, mai makon haka ma abinda ya damesu shiga wadannan ma’aikatan su basu rabonsu na harajin da suka tara da zalunci.

Babu ruwansu da yadda suka tara kudade wajen mutane, ba ruwansu da yawan kudaden da suke karba a hannun mutane a duk fadin kasar.

Mulkin banu umayya ya tabbatar mana da cewa Imam Al-Hassan tare da zaben sulhuntawa da Mu’awiya dan Abusufyan, ya tabbatarwa al-ummar musulmi hakikanin banu umayya musamman Mu’awiya dan Abu sufyan, na irin zaluncin da suka yiwa al-ummar musulmi, har saida hakan ya jawo masu kiyayya a cikin al-ummar har zuwa lokacinda aka kaudasu kwata-kwata a kan kujerar sarauta ko jagorancin al-ummar musulmi.

Kuma abubuwan da suka aikata ya zama tabo babba ga dangin a raye da kuma bayan mutuwa, har duniya ta nade. Sannan iyalan gidan manzon Allah (s) wadanda suke son batar da su kwata-kwata sai kara daukaka suke, sannan musulmi suna kara sanin matsayinsu da kuma irin baiwar da allah yayi masu na iya rayuwa a karkashin ikon mafi munin mutane a tarihin addinin musulunci.

A cikin shirimmu na gaba zamu yi magana dangane da siyasar Ahlul baiti ko iyalan gidan manzon Allah (s) musamman a lokacin mulkin banu umayya, da yadda suka bi da su don ganin basu shafe addinin musulunci daga doron kasa saboda shafe addinin musulunci da kuma lalata addinin ta yadda za’a bar ambatonsa kwata-kwata. Ta yadda za’a bar ambaton manzon Allah (s) a kiransa sallah da kuma girmama shi. Wannan shi ne manufar mu’awiya dan Abusufyan kamar yadda muka bayyana da shirye-shiryemmu na baya.

Allah Ta’ala ya kare addininsa daga gurbata, sannan wandar da iyalan gidan manzon Allah (s) da mabiyansu, saboda su ne masu riko da addinin musulunci na gaskiya har duniya ta nade, kuma har zuwa lokacinda Allah zai daukaka wannan addinin ya fifita shi ya kuma bashi rinjaye kan dukkan addinai kamar yadda yayi al-kawari a karshen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments