Kissoshin Rayuwa: Kissar Fatimah Azzahra(s) 36

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Ayatullahi Shahid Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddin Ruma, ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da kuma a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon Allah (s) kuma mahaifiyar Alhassan da Alhussan da muke kawo maku, mun tsaya a inda muka fara magana dangane da abinda ya zo cikin allon da Jabir dan Abdullahin Ansari ( r) wanda ya gani a hannun Fatimah (s) a lokacinda ya je wajenta don tayata murnar haihuwar Imam Hussain (a).

Mun bayyana cewa Imam Sadik (a) ya ce babbansa Imam Muhammadl Bakir (s) ya kebe da Jabir dan Abdullahil Ansari, inda ya tambaye shi dangane da allon, sannan ya je tare da Jabir zuwa gidansa, inda Jabir ya fito masa da rubutun da ya gani a cikin koren allon a kan wata takardar fata, sannan Imam Bakir (a) ya ce masa ya riki takardar, sannan shi kuma ya karanta masa abinda yake cikinta, sai ya riketa sannan Imam Bakir (a) ya karanta har ya kammala, ba tare da ya saba da abinda yake cikin takardar Jabir ba ko da harafi guda ba.

Sannan mun kawo maku nassan abinda ya zo cikin wannan allon wanda All..T ya bada shi kyauta ga manzon All..(s), sannan shi kuma ya bada shi kyauta ga Zahra (s) don yayi mata Bushara da haihuwar Imam Alhussain (a). Shi dai Jabir ya shigo wajen Fatima (s) ne ya kuma ga allon wanda yake dauke da sunayen wasiyan manzon All..(s) daga yayan Fatima (s) daga kuma yayan Alhussain (a) a hannuta.

A shirimmu day a gabata mun tsaye inda All..T mai girma da dauka yan ambaci, limami na 8, wato Imam Aliyu dan Musa (s) wanda sarki Mamun dan sarki Haruna Rasheed ya kashe shi a toos, ya kuma bisneshi kusa da babansa Harunar rasheed a Mashad. …sannan ya ci gaba da cewa:

Zancen gaskiya daga wajena, ita ce, lalle sai na taimaka masa da dansa Muhammadu, kuma khalifansa a bayansa, kuma magajin ilminsa, shi taskar ilmina ne, kuma ma’abucin sirri na, kuma hujjata a kan halittuna, babu wani bawan da zai yi imani da shi face na sanya Aljanna makomarsa. Sannan na bashi ceton mutane 70 daga cikin danginsa, dukkaninsu wadanda suka cancanci shiga wuta.

Zan cika sa’adata ga dansa Aliyu, waliyyina kuma mai taimaka mani, kuma mai shaida a cikin halittu na, kuma amintacce na a bisa wahyina, zan fito da mai kira zuwa tafarkin Allah daga wajensa, kuma mai taskace ilmina, Alhassan, sannan zan cikita wancan da dansa (Muhammadu) jinkai ga talikai. Yana da kamalar Musa, da kwarjinin Isa, da hakurin Ayyuba, Za’a kaskanta majibantan al-amarisa a zamaninsa, za’a bada kyautar gutsurarrun kawukansu, kamar yadda ake bada kyautar kawukan turkawa da Dailam (a lokacin) kuma za’a kashesu, a kuma kona su, zasu kashence cikin tsoro, suna firgici, masu tsoro, za’a shafe doron kasa da jininsu, kuma bone da wahala za su yawaita cikin matansu, wadannan sune masu jibantan al-amarina na gaskiya.

Da su ne, zan tunkude makauniyar fitina kamar dare mai duhu, albarakashinsu ne zan tunkude girgize-girgizen kasa, kuma zan tunkude guguwowin iska da kuma maramarai. Wadannan! salati su tabbata a garesu daga Ubangiji da kuma Rahamarsa, kuma wadannan sune shiryayyu). Karshen abinda ya zo cikin allon Fatima (s) kenan.

Abdurrahman dan Salim ya ce, Abubasir yace masa: Da baka san wani hadisi sai wannan, da ya wadatar da kai. Ka rikeshi da kyau, kada ka fadawa kowa sai wanda ya cancanci saninsa.

Masu sauraro kun ji irin ilmin da Zahra (s) ta samu daga wajen mahaifinta manzon All..(s). Kunji kuma yadda al-amarinta yake hade da kaddarorin All..T har duniya ta tashi. Musamman sanin shuwagabanni da wasiyyan manzon All…(s) gaba dayansu sun fito ne daga yayanta, sai kuma mijinta.

Amma a dayan bangaren kuma kun ji abinda wasu wadanda basu santa ba ko suka yin kamar basu santa ba, suke fada dangane da ita (s).

Al-Aqqad ya kawo a cikin littafinsa (Fatimah wa Fatimiyun) ya na cewa:…An karbo hadisi daga Hassan dan Hassan daga Fatima (s) ta ce: Manzon Allah (s) ya shiga waje na sai ya ci dafaffen nama, sai Bilal ya kira sallah, sai ya tashi zai yi sallah, sai na rike rigarsa, sai na ce,: Ya babana ba zaka yi alwala ba? Sai yace: Saboda me zan yi alawala ya diyata, sai na ce: daga cin abincin da wuta ya taba shi, sai yace mani: Shin mafi dadin abincinku ba shi ne wanda wuta ya taba ba? .

Al-Aqqad yana son ya nuna Fatimah (s) bata san hatta abubuwan da suke warware alwalaba a cikin wannan hadisin. Banda haka, da wannan hadisin gaskiya ne, ai yakamata ace duk musulmi sun san da shi, tunda hukunci ne da suke bukatar saninsa don kyautata sallarsu.

Ban san daga inda Al-Aqqad ya samo wannan hadin ba, wanda a yanke kariya ce, aka jinginawa shugaban matan duniya. Don a nuna jahilcinta, da hukunce hukuncen shari’a. Ta daukaka daga wannan karyar.

Sai dai abin tambaya ga wadanda suka kirkiro wannan hadisin da kuma wadanda ya burgasu, musamman shi Aqqad da ya kawo shi cikin littafinsa, kuma kamar yana jin dadi da jin wannan hadisin, inda diyar manzon All..(s) bata san hukuncin cewa cin dafaffen nama baya warware alwala ba, shi ne.

Shin daga Ina Zahra (s) take samun ilminta, ba daga wajen babanta ba, da kuma mijinta. Wanda ya kasance kofar ilmin babanta?, ko kuma daga alkur’ani mai girma kai tsaye? To ta yaya aka yi basu sanar da ita wannan hukuncin ba, kuma har ta yi tunanin cewa cin nama ya na warware alwala?.

Idan zaku tuna, a cikin shirye-shiryemmu da suka gabata, munyi maganar cewa idan Zahra (s) ta tsaya a mehrabinta tana salla, sai haskenta ya bayyana ga mala’ikun sama kamar yadda taurari suke bayyana ga mutanen kasa a cikin dare. Ta yaya ta kai wannan matsayin bata san hukunce hukuncen alwala ba? Abin mamaki.

Wannan kadan kenan daga cikin zaluntar da aka yiwa iyalan gidan manzon All..(s) a bayan wafatinsa, inda aka maidasu Jahilai, aka daukaka wasu akansu, aka dauki matsayinsu wanda All..T ya basu aka bawa wasu daga cikin wadanda ba sa dasawa da su.

Mafi yawan al-ummar musulmi sun jahilci matsayin iyalan gidan manzon All..(s) wadanda suke cikinsu, duk da cewa a zahiri suna bayyana sonsu, amma kuma sarakunan da suka gabata, musamman sarakunan Banu Umayya da Abbasiyawa, sun kaskantar da su a cikin wannan al-ummar tare da taimakon malamansu wadanda suka cika littafai da karyayyaki dangane da su. Wanda hakan ya basu damar hawa kan kujerar shugabanci wanda Allah ya basu. Suka kuma nisanta su daga sauran musulmi. Sai suka jahilcesu. Suka takaita da sonsu a baki kawai ba a cikin sauran al-amuran addini ba.

Don haka a cikin hidisin allo, wanda Jabir dan Abdulahin Ansari ya rubuta abinda yake cikin koriyar allon da All..T ya aikowa manzon All..(s) sannan shi kuma ya bada shi kyauta ga diyarsa (s) yana dauke da cewa.

Wasiyan manzon Allah(s) 12 ne a bayansa. Na farkonsi Mijin Zahra(s) Aliyu dan abitalib (a), sannan dansa Alhassan, sannan dansa Alhussain, sannan yaya da jikokin AlHussain 9. Har ila yau a cikin allon ya kawo sunayensu daya bayan daya, wasu har da lakubansu. 

Aliyu bin Hussain Zainul Abidin, Muhammad bin Ali wanda akewa lakabi da Bakir, sannan Jaafar dan Muhammad Assadik (s), sannan dansa Musa dan Jaafar Alkzim(s), sannan dansa Imam Aliyu dan Musa Al-Ridha(a), wanda yake kwance a garin Toos, sannan dansa Muhammadu Al-jawad (s), sannan dansa Aliyu dan Muhammad Attaki(s), sannan dansa Hassan dan Ali Alaskari (s), sannan dansa mai suna Muhammad dan Hassan.

A Karshen hadisin ya bayyana cewa mabiyan limami na 12 zasu sha wahala, amma saboda su ne Allah Ta’ala yake tunkude musibu da dama daga mutanen kasa. Sannan a wasu hadisan, shi ne All..zai mallakarwa kasa gaba dayanta, ya cikata da adalci bayan cikarta da zalunci a karshen zamani. Wadannan sune wasiyyan manzon All..(s) daga diyarsa Fatima Azzahra (s).

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a ciki shirimmu na  yau sai kuma wata fitowa idan Allah ya kaimu, wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments