Kissoshin Rayuwa: Kissar Fatimah Azzahar (s) 37

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawai na maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun tsaya a idan muka yi magana dangane da hadisin ‘Allo’, wato hadisin Allon da manzon All..(s) ya karba daga All..mai girma da daukaka, dangane da wadanda zasu gajeshi a bayansa ko wasiyyansa. A cikin allon akwai sunanyen dukkan wasiyansa 11, dukkansu daga yayan Fatimah (s), na farkonsu mijinta Aliyu dan Abitalib(a) sannan sauran yayansu da jikokinsu 11.

Munji yadda Jabir dan Abdullahil Ansari (r) daya daga cikin sahaban manzon All..(s) ya je wajen Fatima (s) don ya taya ta murnin haihuwar Alhussain (a) sai ya ga allo koriya a hannunta (s) sannan ya tambayeta dangane da shi, sai ta fata masa cewa sunayen babanta da mijinta da kuma yayanta ne wasiyyan manzon All..(s) ke cikin allon. A nan ne sai ta mikawa Jabir allaon wanda ya karanta abinda yake ciki ya kuma rubuta shi a kan wata takardar fata tasa.

Takardan tana wajentasa har zamanin Imam Bakir (s) limamni na 5 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All.(s), wanda ya tambayeshi dangane da takardar, ya kuma nuna masa shi. Imam Muhammad Bakir (s) ya karanta takardan da ke hannun Jabir ba tare da yana karatu kai tsaye daga cikinta ba.

Ya kuma kammala ba tare da ya sauya ko harafi gudu na takardan Jabir ba.

Sannam mun bayyana cewa a cikinta akwai sunanyen su, wadanda suka hada da Aliyu, Alhassan, Alhussain, Aliyu dan Hussain, Muhammad dan Ali, Ja’afar dan Muhamma, Musa dan Ja’afar, Aliyu dan Musa, Muhamad dan Aliyu, Aliyu dan Muhammada, Hassan dan Aliyu da kuma Muhammad dan Hassan, wanda shi ne Iimami na 12 wanda kuma akewa lakabi da Mahdi(a). Kuma shi ne All..ya yiwa alkwarin cika duniya da adalci bayan cikarta da zalunci.

Sannan mun ji yadda wasu musulman suke kasksantar da ita (s), suna ruwaito hadisai wadanda suke nuna jahilcinta da abu mafi sauki a ilmin addini, wato hukunce–hukunce alwalah, ba tare da kula da matsayinta ba suna kawo su cikin littafannsu.

A cikin shirimmu na yau zaku ji yadda Fatimah (s) take himmatuwa da Hijabin Musulunci, wanda ya kasance babbar kariya da mutunci da hakkin mata musulmi.

Addinin musulunci ya himmatu da hijabin ko surturan addinin musulunci ga mata, kuma ta wannan ne yake kare mutunci da kuma duk abinda zai cutar da mace a cikin rayuwar zamantakewa.

Zahra (s) ta san cewa dubban cututtuka masa addabar mata suna cikin barin Hijabi da kuma bayyana kawarsu ga wasu mazaje ne.

Kamar yadda yake a fili a wannan zamanin. Duk wanda yake son sanin irin musibar da mata suke ciki a wannan zamanin, ya karanta jaridu da mujallu na ko wace kasa daga cikin kasashen musulmi ko sauran kasashen duniya. Zai ga matsaloli daban daban, kama daga fiyade, walakanci, kaskanci, zubar da ciki, kashe jarirai, kha’incin mata ga mazajesu, ka’incin maza ga matansu, watsewar iyalai, ko rashin dadewar aure, da kuma sabon Allah da yawan zunubbai tsakanin maza da mata duk saboda kauracewa hujiban musulunci da kuma rashin boye jikin ga sauran mutane wadanda ba mazajensu ba.

Kowa ya tabbatar a duniyarmu a yau ana aikata miliyoyin laifuffuka wadanda suke da dangantaka da bayyana jikin mata ga wadanda ba mazajensu ba. Kuma idan ka dubi baya a lokacinda mata suke suturce jikinsu ga sauran Mazaje, ba sa fuskantar irin wadannan matsaloli saboda ba sa yaye jikinsu ga sauran mazaje.

A lokacinda ta bar wadannan halaye ne, ta kauracewa hijabi wadannan musibi suka sauko kanta, ta zama bata da mutunci a gaban mazaje muharramanata daga cikin musulmi da kafirai. Wannan halin zai ci gaba mutukar wannan halin na kauracewa hijiban musulunci ya ci gaba  

Ga wasu hadisai wadanda suka bayyana yadda manzon All..(s) ya bayyana jin dadinsa da abinda yaji daga diyarsa Zahra(s) dangane da hijabi da kame kai ga mata musulmi.

Abu-Na’im ya kawo a cikin littafinsa  Hilyatul Awliya JZ 2 SH 40, daga Anas dan Malik yana cewa: Manzon All..(s) ya ce: Menene mafi Alkhairi ga mata? Bamu san abinda zamu fada ba, sai Aliyu (a) ya je wajen Fatimah(s), ya tambayeta, sai ta ce: Ba zaka ce masa, abunda ya fi alkhairi garesu shi ne kada su ga mazaje ba, kada kuma su gansu ?. Sai Aliyu (a) ya dawo ya fada masa. Sai manzon All..(s) ya ce: Ta yi gaskiya, ita tsokace daga gareni.

A cikin wata ruwayar, Aliyu (a) ya cewa Fatimah(s), menene mafi alkhairi ga Mata? Sai tace: Kada su kalli mazaje kadu mazaje su kallesu. Sannan aka fadawa manzon All..(s) abinda ta fada, sai ya ce: Ai abin sani kawai Fatimah bangare ne daga gareni.  

Ibn Maghazili ya kawo cikin littafinsa ‘Almanakib daga Imam Aliyu dan Hussain dan Ali (a) yana cewa, wata rana wani makaho ya nemi izinin shiga wajen Fatima diyar manzon Allah (s), sai ta tashi ta sanya Hijabinta, sai manzon All..(s) yace, mata: Me yasa kika sanya hijabi?, ai shi makaho ne, sai tace: Ya manzon All..idan baya kallona, ni ina kallonsa. Kuma yana jin kanshi, sai manzon All..(s) ya ce: Na shaida ke wani bangare ne daga gareni.

Yanzun kuma bari mu dubi addu’o’in Zahra(s), wadanda suke daga cikin manya-manyan addu’o’i wadanda idan musulmi ya yi riko da su ba zai taba tabewa ba.

Ko wa ya san cewa ita addu’a, ana yinta a duk lokuci, ba sai wani abu ya sami mutum  sai ya koma kan addu’a ba. Dole ne ya zama mutum yana da wasu lazimai da addu’o’i wadanda yake yinsu safe da maraishe a cikin zaman lafiya ko tashin hankali da wahala.

Wannan yana taimakawa mutum ya zama a ko yaushe yana tare da Allah. Don haka an ruwaito hadisai da dama daga Fatimah (s) na irin addu’o’in da take yi, ta kuma luzumcesu a duk tsawon rayuwarta. Addu’o’i wadanda mahaifinta manzon All..(s) ya sanar da ita.

A cikin littafin Muhajud-da’awaat na sayyid bin Tawoos, daga Imam Hassan daga Aliyu dan Abitalib (a) daga mahaifiyarsa Fatimah (s) ta ce: Manzon All..(s) ya ce mata: Ya diyata ba  zan sanar da ke wata addu’a wacce ba wanda zai yi addu’a da ita ba, face an amsa addu’arsa?. Sannan asiri ba zai taba kama shi ba, hakama guba, kuma makiyi ba zai taba walakantashi ba, shaitan ba zai bijiro masa ba, kuma mai jinkai (Allah) ba zai yi watsi da shi ba, zuciyarsa ba zai karkata daga hanya ba, kuma Allah ba zai maida addu’arsa ba, kuma za’a amsa dukkan addu’o’insa gaba daya.?

Sai tace: Ya manzon All..wallahi wannan ya fi soyuwa a gareni, fiye da duniya da abinda ke cikinta.

Sai yace ki ce:

( Ya a’azzu mazkurin, … har zuwa karshen addu’ar. Don tana da tsawo ba zamu iya kawo ta gaba daya ba.) ..har zuwa inda ya ce mata: Sai a ce maki, na’am, na’am.

A kwai wata addu’a wacce ta shahara a cikin mabiya iyalan gidan manzon Allah(s)  wato shi’a, wacce ake kira Du’a’un Noor, wacce kuma take maganin zazzabi, kamar yadda mutane da daga suka jarraba.

Sayyid bin Tawoos ya kawo cikin littafin Muhajud Da’awad. Takaitaccen hadisin shi ne,  Zahra (s) ta koyawa salman Alfarisi wannan addu’ar, tace masa idan kana son kada cutar zazzabi ta kamaka matukar kana raye a nan duiya, ka luzumci wadannan kalmomi wadanda mahaifina Muhammadu (s) ya sanar da ni, kuma na kasance ina karantata safe da maraice.

Da sunan All..Mai rahama mai jinkai.

Da sunan Allah haske, da sunan Allah hasken haske, da sunan Allah haske bisa haske, da sunan Allah  wanda shi ne mai jujjuya al-amura, da sunan Allah wanda ya halicci haske daga haske. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci haske daga haske, ya kuma sauko da haske kan dutsen Toor, cikin littafi rubutacce, cikin takarda wanda aka bude  shi, gwargwadon bukata kuma takaitacce, bisa annabi mai abin tawadar rubutu, godiya ta tabbata ga Allah wanda ake ambata da daukaka, da kuma alfakhari wanda ya shahara, kuma abin godiya a cikin sauki da tsanani, kuma Allah yayi salati  bisa shugabammu Muhammadu da kuma iyalan gidansa tsarkaka.)

Salman yace: Na rantse da Allah na sanar da mutum sun fi dubu a Makka da Madina wadanda suke fama da zazzabi sun warke da izinin Allah.

Add’uo’in da aka ruwaito daga Zahra (s) suna da yawa, amma zamu takaita da wannan.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan Allah ya kaimu wassalamu alikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments