Kharrazi: Iran Za Ta Iya Canza Akidarta Ta Soji Idan Ta Fuskanci Barazana Ta Wanzuwa

Shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na Iran ya ce mai yiyuwa ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta kara yawan makamanta masu linzami,

Shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na Iran ya ce mai yiyuwa ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta kara yawan makamanta masu linzami, yana mai gargadin cewa kasar za ta iya sauya duk akidarta ta soja, idan ta fuskanci wata barazana ta wanzuwa.

“Idan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fuskanci wata barazana ta wanzuwa, to babu makawa za mu canza manufofin akidarmu ta  soji,” in ji Kamal Kharrazi a wata hira da tashar talabijin ta al-Mayadeen ta Lebanon.

Ya jaddada cewa Iran tana iya kera makaman kare dangi, amma abin da ya hana hakan shi ne fatawa da hukuncin addini, wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayar kan makaman kare dangi.

“Yanzu muna da damar da ake bukata don kera makaman nukiliya, kuma abu daya tilo ne ya hana hakan, shi ne fatawar Jagora da ta haramta kera makaman nukiliya.”

Dangane da nau’in makami mai linzami na Iran, Kharrazi ya ce, “Ya zuwa yanzu mun gwada hankalin kasashen yammacin turai, tare da ba su dama domin yin abin da ya dace, Amma idan ba su yi la’akari da hakan ba, musamman dangane da batun kare yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, babu wani dalili da zai sa mu ci gaba da yin la’akari da hankulansu, za mu yi abin da ya dace maslahar kasarmu da al’ummarmu.”

“Saboda haka, akwai yuwuwar yawan makamai masu linzami na Iran zai karu matuka.”

Da yake tsokaci game da hare-haren da Isra’ila ta kai kan wuraren soji a Iran, Kharrazi ya ce “tabbas kasar za ta mayar da martani a daidai lokacin da ya dace.”

Ya nanata cewa Iran ba ta da sha’awar ganin cewa wanann yaki ya yadu zuwa sauran yankuna na gabas ta tsakiya, amma kuma a lokaci a shirye take ko da hakan ta kasance.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments